Jam'iyyar LDP na shirin komawa mulki a Japan

Shinzo Abe, jagoran jam'iyyar LDP a Japan
Image caption Shinzo Abe, jagoran jam'iyyar LDP a Japan

Sakamakon jin ra'ayi a Japan na nuna cewa jam'iyyar LDP ta masu matsakaicin ra'ayin rikau da ta dade tana mamaye da harkokin mulki, amma kuma ta sha kaye a zabe shekaru uku da suka wuce, a yanzu tana shirin komawa kan karagar mulki.

Masako Sasaki wata wadda ta kada kuri'a, ta zargi Jam'iyyyar Democratic da rashin cika alkawurran da dauka , don haka naka ta juya ma ta baya a wannan karon.

Sakamakon na nuna cewa jam'iyyar ta LDP zata samu babban rinjaye, ita kuma jam'iyyar Democratic wadda ta samu gagarumar nasara a zaben 2009 zata sha mummunan kaye.

Hakan shi zai sa jagoran jam'iyyar ta LDP, Shinzo Abe, mai ra'ayin rikau, dake goyon bayan mallakar makaman nukiliya, sake zama praminista a karo na biyu.

Ya sha alwashin daukar tsauraran matakai a kan kasar China.

A baya Mr Abe ya taba musanta zargin cewa dakarun kasar Japan sun rika tilasta ma mata a kasar China yin lalata da su, a lokacin Yakin Duniya na Biyu. Dangantaka tsakanin China da Japan dai da ma ta tabarbare, yanzu kuma akwai alamun zata kara sukurkucewa.