'Sakaci ne ya janyo gobarar masana'anta a Bangaladesh'

Gobarar Bangaladesh
Image caption An kammala binciken musabbabin gobarar Bangaladesh

Kwamitin binciken wanda gwamnatin Bangladesh ta kafa ya kammala da cewa gobarar wadda ta tashi a masaƙar Tazreem a watan da ya gabata, ta faru ne bisa ganganci.

Sai dai shugaban kwamitin binciken Main Uddin Khandaker ya shaidawa BBC cewa har ya zuwa yanzu ba za su iya cewa takamamme ga wanda ya haddasa gobarar ba.

Ma'aikata fiye da 110 ne su ka rasa rayukansu yayin da gobarar ta mamaye ginin masana'antar wanda ke wajen birnin Dhaka.

Ƙasar Bangladesh ita ce ta biyu a duniya wajen safarar ɗinkakkun tufafi, baya ga ƙasar China.