Yau ranar hutun jimami a jihar Kaduna

Taswirar Jihar Kaduna
Image caption Taswirar Jihar Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta bayyana yau litinin a matsayin ranar hutu domin jimamin mutuwar gwamnan jahar Mista Patrick Ibrahim Yakowa.

Za a kuma kwashe kwanaki bakwai tun daga jiya zuwa ranar 23 ga wannan watan ana zaman makokin rasuwar gwamnan.

Tsohon gwamnan ya mutu ne a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Bayelsa a ranar Asabar din data gabata.

Tuni dai aka rantsar da mataimakin marigayi Yakowan, Mukhtar Ramalan Yero a matsayin sabon gwamnan jihar.