Libya ta rufe kan iyakokinta ta kudanci

Dakarun kasar Libya
Image caption Dakarun kasar Libya

Kasar Libya ta rufe kan iyakokinta dake kudancin kasar kana ta bayyana wasu larduna bakwai dake kudanci, a matsayin yankunan soji saboda fargabar rashin tsaro.

Wani mai magana da yawun Majalisar dokokin kasar ya ce an dauki wannan mataki ne don shawo kan matsalar bakin haure da wasu kayayyaki dake kwararowa cikin kasar.

Ana dai kyautata zaton cewa wannan matakin na wucin gadi ne, kafin a fitar da sabbin ka'idoji.

Sai dai Majalisar dokokin bata sanar da tsawon lokacin da kan iyakokin zasu ci gaba da kasancewa a rufe ba.

Wadannan kan iyakokin da aka rufe dai sun hada da kan iyakar kasar da kasashen Sudan, Niger, Chadi da kuma Algeria.

Majalisar dokokin kasar ta bayar da umarnin ne a bisa abin da ta bayyana da wani yunkuri na shawo kan matsalar kwararowar bakin haure da wasu kayyakin da basu kamata ba, ta kan iyakar kasar ta Libya.

Matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci horar da wasu 'yan kasar Libya, kan yadda za su kare kan iyakokinsu na kudancin kasar, domin hana fasa kwaurin makamai ba bisa ka'ida ba daga kasar.

Batun dai -dai ta al'amuran kudancin kasar ta Libya wacce ta samu koma baya tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Kanal Gaddafi, ya kasance wani abin tattaunawa da zazzafar muhawara a Majalisar dokokin kasar.

Larduna kamar su Kufra sun fuskanci mummunan rikici a farkon wannan shekarar, wanda fito na fiton da aka dade ana yi game da hanyoyin da ake bi wajen yin fasakwauri ya haddasa.