An sake zaben Zuma ya shugabanci ANC

ANC
Image caption A taron na ANC, an kada kuri'ar mukamai shida na shugabancin jam'iyyar

An sake zaben shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar ANC.

Zuma ya samu nasara da gagarumin rinjaye a kuri'ar da wakilan ANC 4,000 suka kada a taron jam'iyyar da aka yi a Manguang.

Ya samu nasarar ne duk kuwa da kalubalantarsa da mataimakinsa Kgalema Motlanthe ya yi wajen takarar shugabancin jam'iyyar.

An dai maye gurbin Mr. Motlanthe da dan gwagwarmayar yaki da wariyar launin fatan nan Cyril Ramaphosa, a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Jam'iyyar ta ANC dake mulkin kasar tun bayan kawo karshen mulkin tsiraru a shekarar 1994 ake sa ran za ta lashe zaben shugaban kasan da za a yi a shekarar 2014.

A wani bangaren kuma, an gurfanar da wasu fararen fata hudu masu ra'ayin rikau da ake zargin da hadin baki don sanya bam a taron na ANC

A ranar Litinin ne dai aka kama wadanda ake zargin, a wani samamen da aka yi a fadin kasar.

Kuma ana tuhumarsu da laifin cin amanar kasa da ta'addanci.