Kisan Newtown: Obama na ganawa da jami'ai

  • 18 Disamba 2012
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaba Obama na Amurka ya fara tattaunawa da manyan jami'an gwamnatinsa domin lalubo hanyar tunkarar harbe mutanen da aka yi a garin Newtown na jihar Connecticut.

Kafin hakan dai an yi jana'iza ta farko ta wasu daga cikin yara ashirin da manya shidan da wani dan bindiga ya harbe a makarantarsu ranar Juma'a.

Wannan lamarin dai ya sake tayar da muhawara a kan dokokin mallakar makamai a kasar.

Wani wakilin BBC a Amurkar ya ce ga alama ra'ayoyi sun fara sauyawa, wasu 'yan majalisar dattawa na jam'iyyar Democrat su biyu wadanda a baya ke goyon bayan baiwa kowa damar mallakar makamai sun yi kira da a yi sauyi.

Karin bayani