An kashe ma'aikatan Polio a Pakistan

Kisa kan masu allurar Polio a Karachi
Image caption Cutar Polio ta yi katutu a Pakistan

'Yan bindiga sun harbe wasu mata dake aikin alluran riga kafin cutar shan Inna -- ta Polio a Pakistan.

Hare haren sun faru ne a wasu yankuna 3 daban daban na birnin Karachi mafi girma a ƙasar da kuma a Peshawar.

Jami'an yankin sunce a halin yanzu an dakatar da aikin riga kafin a waɗannan yankuna.

Ba a dai san kowa ya harbe matan ba, to amma a baya shugabannin ƙungiyar Taliban sunce ana amfani da aikin ne domin leƙen asiri, sannan kuma wani ƙoƙari ne na hanawa musulmi haihuwa.

Cutar ta Polio dai ta yi katutu a Pakistan , kuma a makon nan hukumar lafiya ta duniya ta ƙaddamar da wani aiki a dukkanin faɗin ƙasar domin baiwa yara magungunan riga kafin kamuwa da cutar.