'Karancin fetur na barazana ga aikin agaji a Syria'

Image caption Valerie Amos babbar jami'a mai kula da aiyukkan jinkai.

Babbar jami'a mai kula da aikin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta yi gargadin cewa karancin man fetur na barazana ga aikin agaji a Syria.

Valerie ta kuma yi kira ga gwamnatin Syriar ta baiwa Majalisar damar shigar da mai kasar, domin samun kaiwa mutanen da rikici ya rutsa da su kayan agaji.

Jami'ar ta yi kira ga Damascus ta ba da damar kai ma'aikatan agaji, ta kuma kyale wasu kungiyoyin bada agaji goma su yi aiki a kasar.

Baroness Amos dai na yiwa kwamitin tsaro na Majalisar bayani ne kan ziyarar da ta kai kasar kwanan nan.

Shi ma farayin ministan Syria Wael al Halaki a wata ziyara da ya kai birnin Aleppo, ya ce ana fuskantar karancin mai fetur da ke haddasa tsaikon isar kayayyaki agaji yankin.

Yace an tanadi isassun kayayyakin amfani da man fetur, amma matsalar ita ce ta yadda za su isa ga muhallin mabukata, saboda kafar ungulun da 'yan tawaye ke yi.

Karin bayani