Ana zaben shugaban kasa a Korea ta Kudu

Image caption Masu zaben na jefa kuri'unsu cikin akwati a wata rumfar zabe dake Nonsan,

Al'ummar Korea ta kudu na jefa kuri'a ranar Laraba domin zaben sabon shugaban kasa.

Masu zabe sun bijirewa tsananin sanyin da ake fama da shi, sun fito runfunan zabe, inda ake sa ran a samu fitowar jama'a sosai

'Yar takarar jam'iyya mai mulki, Park Geun-hye, wacce 'ya ce ga wani tsohon shugaban mulkin soja, na karawa da Moon Jae-Hin, wani tsohon lauya mai kare hakkin bil'adama, wanda aka taba tsarewa saboda adawarsa ga mahaifin wadda yake kalubalanta.

Dukansu sun ce za su sake farfado da shirin tattaunawa da Korea ta Arewa amma ra'ayoyinsu sun sha bamban kan lokacin da ya kamata ayi hakan.

In har ta yi nasarar lashe zaben, Park Geun-hye ce za ta kasance mace ta farko da ta shugabanci al'ummar Korea ta kudu.

Karin bayani