An rage ayyukan rigakafin polio a Pakistan

Ana diga wa wani yaro maganin rigakafin polio
Image caption Wasu 'yan bindiga ne a kan babura suka bude wuta ga ma'aikatan rigakafin cutar shan inna a Pakistan.

Majalisar Dinkin Duniya ta rage ayyukanta na yaki da cutar shan inna ko Polio a Pakistan, bayan harbe wasu ma'aikata biyu.

Harin dai ya auku ne a yankin Penshawar, inda aka kashe wata mai kula da masu rigakafin cutar da kuma direbanta, sannan wani dalibi mai aikin sa kai ya jikkata.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma kungiyar Taliban ta yi barazanar kai harin adawa da ayyukan yaki da cutar ta shan inna da majalisar Dinkin Duniya ke yi a kasar.

Kisan na zuwa ne kwana daya bayan an harbe wasu mata biyar ma'aikan rigakafin na polio a ranar Talata.

Majalisar ta ce za ta janye ma'aikatan polio daga kan titunan kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ce ke daukar nauyi tare da bada kayan aiki ga masu aikin rigakafin cutar ta shan inna a Pakistan.

Sai dai duk da kisan, jami'an kasar sun ce za a cigaba da ayyukan rigakafin cutar a wasu guraren, kodayake wasu ma'aikatan tuni suka fara kin fita aikin na rigakafin, acewar kamfanin dillacin labarai na Reuters.

Kasar Pakistan dai na daga cikin kasashe uku na duniya da har yanzu ke fama da cutar ta shan inna.