An sace 'yan kasar India biyar a Najeriya

Wasu mayakan sa kai a yankin Niger Delta Nijeriya
Image caption Wasu mayakan sa kai a yankin Niger Delta Nijeriya

A Najeriya wasu 'yan fashin kan teku a yankin Niger Delta sun kama wani jirgin ruwan dakon mai na kamfanin Medallion Marine mai suna SP Brussels.

'Yan fashin sun kama jirgin tare da yin garkuwa da wasu ma'aikatansa da ake kyautata zaton 'yan kasar India ne , su biyar.

Fashin jiragen ruwa, da yin garkuwa da mutane abubuwa ne da suka zama ruwan dare a mashigin ruwan Guinea, yankin da ake cewa shi ne na biyu baya ga Somalia inda aka fi fuskantar hadarin 'yan fashin kan teku.

Wannan lamari ya sa kudin inshora ya kara tsada.

Ko a ranar Litinin ma wasu 'yan bindiga suka kama wasu ma'aikatan kamfanin Kyundai na kasar Koriya ta kudu a Najeriyar.