'Jami'an Amurka na da laifi a harin Benghazi'

Image caption Ofishin Jakadancin Amurka a Benghazi bayan kai masa hari

Wani kwamiti mai zaman kansa da ke binciken harin da aka kaiwa ofishin Jakadancin Amurka dake Benghazi ranar 11 ga watan Satumba wanda ya halaka Jakadan kasar ta Amurka da wasu mutanen uku, ya gano cewa gazawar jami'an ma'aikatar harkokin wajen kasar ce ta haddasa tsananin rashin tsaro a ofishin.

Kwamitin ya dora laifin kai harin a kan Sashen kula da tsaron ofisoshin diplomasiyyar Amurka da kuma Ofishin kula da al'amuran Arewacin Afirka na ma'aikatar, yana cewa akwai rashin hadin kai da kuma rudani a tsakaninsu game da tsaron Ofishin Jakadancin da ke birnin Benghazi.

Kwamitin da ya bayyana cewar sabanin labaran da aka bayar da farko, babu wata zanga-zanga da aka yi a wajen ofishin jakadancin kuma yace alhakin kai harin na kan wadanda ya kira 'yan ta'addar da suka kai hari kan ofishin.

Ko da yake a lokacin da abin ya faru, jami'an gwamnatin kasar sun danganta shi da zanga-zangar nuna rashin amincewa da wani Fim na cin zarafin addinin musulunci da aka yi a Amurka wadda a ka faro daga birnin Alkahira a wannan ranar.

Amincewa

Rahoton Kwamitin na Accountability Review Board ya kuma ce daukin da gwamnatin Libya ta kai shi ma yana da nakasu kwarai da gaske kuma ya soki manyan jami'an ma'aikatar harkokin wajen Amurkar da kasa daukar mataki ga damuwar rashin tsaro da ma'aikatan diplomasiyyar Amurka dake Libya suka nuna tun kafin a kai harin.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton tace ta amince da sakamakon binciken kwamitin mai zaman kansa wanda ya dora laifin harin kan ma'aikatar ta.

Clinton ta fada a cikin wata wasika da ta aikewa kwamitocin majalisar dokokin kasar cewa ta umarci ma'akatar ta ta da ta aiwatar da sakamakon binciken cikin sauri kuma ga baki dayansa, kuma ta bayyana wasu jerin matakan da za'a dauka domin kyautata sha'anin tsaro a ofisoshin diplomasiyyar kasar.

Ta ce Amurka za ta aike da daruruwa sojojin da za su rika fakon ofisoshin, ta nemi karin kudi domin inganta tsaro da kuma nada wani sabon jami'in da zai rika sa Ido kan ofisoshin da ke wurare masu hadari.

Ga alamu dai wannan rahoton ya bude wani sabon babi gameda harin na Benghazi, wanda a cikinsa aka kashen jakadan Amurka a Libya Chris Stevens, da wani kwararre kan harkokin watsa labarai Sean Smith da tsoffin sojin kundunbalar na Amurka Glen Dorhety da Trone Woods- wadanda ke yiwa hukumar lekan asirin Amurka ta CIA aiki.

Stevens dai shine jakadan Amurka na farko da aka kashe tun a shekarar 1988.

Karin bayani