Benghazi: Jami'an Amurka sun yi murabus

Image caption Hilary Clinton, Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka

Manyan jami'an tsaron Amurka sun sauka daga mukamansu bayan da wani rahoto ya yi kakkausar suka a kan rashin wadatattun matakan tsaro a ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Benghazi na Libya.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen, Victoria Nuland ta fada a cikin wata sanarwa cewa babban jami'i mai kula da tsaron ofisoshin jakadanci Eric Boswel ya yi murabus nan take ranar Laraba, yayin da aka sallami wasu jami'an su uku da bata bayyana sunayensu ba.

An kashe jakadan Amurka da wasu mutanen uku lokacin da wasu mutane dauke da makamai suka farwa ginin da ofishin yake a watan satumba.

Rahoton na wani kwamiti mai zaman kansa ya yi suka a kan gazawar jagororin Ma'aikatar ta Harkokin Waje, sannan ya dora alhakin faruwar al'amarin a kan abin da ya kira matukar karancin matakan tsaro.

Hilary Clinton ba ta da laifi

Ga alamu dai lamarin na Benghazi zai iya shafawa wa'adin shekaru hudun da Hilary Clinton ta yi a zaman sakatariyar harkoki wajen kasar kashin kaji.

Ko da yake rahoton bai nuna mata yatsa kai tsaye ba, hakama jami'an da suka shugabanci kwamitin suma ba su dora mata laifi ba.

Shugaban kwamitin Ambassada Thomas Pickering yace kwamitin ya yi matsayar cewa alhakin sakaci da sha'anin tsaron da aka samu a ofishin na Bengazi na kanana jami'ai ne bana ofishin Mrs Clinton bane.

An dai yi tsammanin Mrs Clinton za ta bayyana wajen wani taron jin ra'ayoyin jama'a kan lamarin na Bengazi da za a yi yau Alhamis, amma yanzu wasu manyan mataimakan ta biyu ne za su wakilce ta; saboda tana murmurewa ne daga fizgar jiki, zubewar ruwan jiki da kuma murdar ciki da tayi fama da su.

Hilary Clinton wadda ke niyyar sauka daga kan mukaminta nan da watan janairu, tace za ta aiwatar da dukkanin shawarwarin da kwamitin ya bayar cikin har da tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin Amurka da ke kasashen waje.