An kashe mutane 39 a tashin hankali a Kenya

kenya
Image caption An kona gidajen mutane a kauyen Tana

'Yan sanda a Kenya sun ce an kashe a kalla mutane 39 bayan wata tarzoma ta barke a kudancin kasar.

A wani kauye dake yankin Tana, ne aka kai hari, inda mutane dauke da adduna da kuma wasu makamai suka farwa mazauna garin, sannan kuma suka bankawa gidaje wuta.

Tuni dai aka tura 'yan sandan kwantar da tarzoma a yankin dake fama da rikicin kabilancin inda a watan Augustan da ya gabata aka kashe sama da mutane dari.

Yawancin wadanda aka kashe mikiyayen kabilar Orman ne kuma suna yawan samun rikici ne da monaman kabilar Pakoma a kan gonaki da kuma ruwa.

Wakilin BBC ya ce "ganin an samu damina mai albarka a bana, akwai wandanda ke ganin rikicin baya-bayanan na da alaka da siyasa saboda shirin zaben kasa da za'a yi a a watan Maris din badi".