Sanata John Kerry zai maye gurbin Hillary clinton

Sanata John Kerry
Image caption Sanata John Kerry zai canji Hillary Clinton

Shugaba Obama ya mika sunan Sanata John Kerry a matsayin wanda zai rike mukamin sakataren kula da harkokin wajen Kasashen Amurka inda zai maye gurbin Hillary Clinton

Mr Kerry shine shugaban kwamitin kula da harkokin Kasashen waje na majalisar dattawan Amurka, kuma shine dan takarar Shugabancin Kasar Amurkan karkashin jam'iyyar Democrat a shekarar 2004

Ba a tsammanin nadin Mr Kerry zai fuskanci wata adawa daga 'yan jam'iyyar Republican

Babban abinda zai maida hankali akai dai shine batun Syria da kuma janyewa daga Afghanistan da kuma batun shirin nukiliyar Iran

Karin bayani