''Mutane 55 sun nutse a tekun Somaliya''

Image caption Gabar tekun Somaliya wuri ne da kuma aike yawan fashi a teku

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane hamsin da biyar 'yan kasar Somalia da Habasha ne ake tsoron sun rasa rayukansu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a gabar tekun Somalia.

Wakiliyar BBC ta ce Majalisar Dinkin Duniyar ta ce kwale-kwalen wanda ke cike makil ba masaka tsinke, ya fada cikin hadari ne jim kadan bayan ya bar tashar jiragen ruwa ta Bossasso da ke arewa maso yammacin Somalia.

Kifewar kwale-kwale da kuma mutuwar 'yan gudun hijira abu ne da ya zama ruwan dare a sashen tekun da ke tsakanin Somalia da Yemen.

Dubun dubatar 'yan kasashen gabashin Afrika ne ke ketare tekun duk shekara, don gujewa tashe-tashen hankula, da kuncin rayuwa, da sauran wahalhalu.

Karin bayani