An bayar da iznin tura soji zuwa Mali

Image caption Zaure kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da iznin amfani da matakin soji don kwato arewacin Mali daga hannun 'yan tawaye masu kishin Islama da ke da alaka da kungiyar Al-qa'ida.

Sai dai kuma ya bukaci a fara samun ci gaba wajen sasantawa a siyasance, da gudanar da zabe da kuma horar da sojoji da 'yan sandan Afrika kafin daukar matakin.

Wani kuduri da kwamitin, wanda shi ne mafi karfin iko a Majalisar ya amince da shi, ya jadadda cewa dole ne a samar da wani tsari mai kaifi biyu, na siyasa da na soji, domin a sake dinke kasar, wadda ta kasance cikin tashin-tashina tun a watan Maris.

Bayan jefa kuri'ar amincewa da kudurin, Ministan Harkoki Wajen Mali Tieman Coulibaly ya ce ''Mali tana cike da farin ciki da amincewa da wannan kudurin wanda ya nuna himmatuwar al'ummar kasa-sa-kasa wajen taimaka mata a gwagwarmayar da take yi da ta'addaci da kuma aikata laifuka, wadanda ke barazana ga zaman lafiyar yankin.''

Sai dai kwanannan Jami'i mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Herve Lasdous ya ce ba ya sa ran ba za a soma amfani da karfin soji kan arewacin na Mali har sai watan Satumba ko Oktoba na shekara mai kamawa.

Shi ma jakadan Faransa a Majalisar Gerard Araud ya shaidawa 'yan jarida cewar yayi sauri a ce ga lokacin da za a soma amfani da karfin sojin saboda sojojin Afrika da na Mali na bukatar a fara basu horo; abubuwa da yawa sun dogara kan shirin siyasa da yanayin kasar maras kyau.

Karin bayani