Amurka za ta iya shiga tsaka-mai-wuya

Image caption John Boehner kakakin majalisar dokokin Amurka.

Yunkuri na baya-bayan nan na kaucewa abin da ake kira tsaka mai wuya ta fuskar tattalin arziki a Amurka--wadda masana da dama suka ce tana barazanar jawowa kasar koma-bayan tattalin arziki--ya ci tura.

A Majalisar Wakilai an yi watsi da kada kuri'a a kan wani kudurin doka da 'yan jam'iyyar Republican suka gabatar wanda ya tanadi karin kudin harajin da masu samun abin da ya haura dala miliyan daya a shekara za su rika biya.

Kakakin Majalisar, John Boehner, ya ce kudurin dokar bai samu goyon baya ba.

A farkon sabuwar shekara wani jerin matakan tsuke bakin aljihu da karin kudaden haraji zai fara aiki a kasar ta Amurka.

Karin bayani