'Yan fashi a Kenya sun yi awon gaba da dabbobi

Kenya
Image caption Rashin tsaro a Kenya

Rahotanni daga Kenya sun ce wasu 'yan fashi sun kai hari wani kauye dake kusa da garin Baragoi dake arewa maso yammacin kasar, inda sukai awon gaba da daruruwan dabbobi.

Ance kimanin 'yan fashin dari biyu ne su ka je yawanci dauke da muggan makamai.

Mutane da dama sun tsere daga kauyen.

Sama da 'yan sanda arba'in ne wasu barayin shanu su ka kashe a garin Baragoi din a watan Nuwanba.

A ranar Juma'a majalisar dokokin Kenyan ta nemi gwamnati ta kafa wata hukumar da zata gudanar da bincike kan kisan 'yan sanda, wanda shi ne mafi muni a tarihin kasar.

Karin bayani