An dawo da zurga zurgar jiragen kasa a Najeriya

Layin dogo
Image caption Layin dogo

A karon farko cikin shekaru da dama an dawo da zurga zurgar jiragen kasa tsakanin Lagos dake kudanci zuwa Jihar Kano dake arewacin Najeriya.

Jirgin farko ya bar birnin Lagos ne a ranar Juma'a da rana, yayin da ya isa birnin Kano ranar Asabar da daddare.

Hukumomi sunce daga yanzu za'a rika jigilar mutane da kayayyaki da kuma man fetur daga kudancin kasar zuwa arewaci.

Masu lura da al'amura dai sun bayyana cewa matukar hakan ya dore, zai taimaka wajen rage yawan haduran motoci baya ga rage yawan lalacewar hanyoyi sakamakon daukar kaya masu nauyin gaske da motocin ke yi.