Gwamnatin Najeriya na `dari-`dari kan bincike hadarin jirgin sama

Hadarin jirgin sama a Najeriya
Image caption Hadarin jirgin sama a Najeriya

A Najeriya, bangaren shugaban kasar na dari-dari da yunkurin da majalisun dokoki da kuma kungiyar gwamnonin kasar ke yi na gudanar da bincike a kan musabbabin hadarin wani jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi sanadiyar mutuwar tsohon gwamnan jihar Kaduna Mr Patrick Ibrahim Yakowa da tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, janar Andrew Azazi da wasu mutane hudu a makon jiya.

Tun bayan aukuwar hadarin ne shugaban kasar ya ce za'a binciki lamarin, amma daga baya sai Kungiyar gwamnonin kasar ta ce za ta so shiga kwamitin binciken a matsayin 'yar kallo, yayin da majalisun dokokin kasar su ma suka kudiri aniyar gudanar da nasu binciken.

Sai dai bangaren shugaban kasar na da ra'ayin cewa rudani zai iya shiga cikin binciken idan hannu ya yi yawa.

Masu sharhi akan al'amura a Najeriyar dai na ganin cewa tilas hukumomi su dauki kwararan matakai matukar ana son kawo karshen aukuwar hadurran jiragen sama dake neman zama tamkar ruwan dare a kasar.