'Yar sanda ta bindige ba-Amurke a Kabul

Hoton mata 'yan sanda a Afghanistan
Image caption Hoton mata 'yan sanda a Afghanistan

A wani lamari da shi ne irinsa na farko, wata jami'ar 'yan sanda a Afghanistan ta kashe wani abokin aikinta dan kasashen yammacin duniya.

Jami'ai sun ce matar mai suna Nargis ta bindige har lahira wani jami'i ba Amurke a hedkwatar 'yan sandan kasar matukar tsaro dake birnin Kabul.

Ana ci gaba da yi ma ta tambayoyi, tare kuma da gudanar da bincike.

A wani lamarin na daban a lardin Jowzjan wani dan sanda ya bude wuta kan abokan aikinsa inda ya kashe shidda daga cikinsu.

Jami'ai sun ce ya tsere da makaman wadanda ya kashen, ya kai wa Taliban.

Birgediya Janar C Madower shi ne kakakin dakarun kasashen wajen, ya kuma ce , wadannan abubuwa ne da suka saba gani, kuma suna aiki tare da abokan aikinsu na Afghanistan, domin kawo karshensu.

Karin bayani