Mallakar bindiga matsala ce a Amurka

Bindiga a kan tutar Amurka
Image caption Bindiga a kan tutar Amurka

An kashe wasu ma'aikatan kashe gobara biyu, aka kuma raunata wani, lokacin da aka bude masu wuta, bayan sun kai dauki sakamakon wata gobara da ta tashi a jihar New York ta Amurka.

Jami'ai sun ce an yaudari ma'aikatan kashe gobarar , wadanda ma'aikata ne na sa -kai suka je inda wutar ta tashi, a garin Webster.

An taras da dan bindigar a mace, da raunin bindiga a kansa.

An yin wadannan harbe harbe ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama game da dokar mallakar bindigogi a Amurka, bayan kisan gillar da aka aikata a wata makaranta a jihar Connecticut, a farkon watan nan.

Karin bayani