'Mandela yana cikin kumari'

Nelson Mandela
Image caption Mandela ya yi bikin kirsimati a asibiti

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce ya samu tsohon shugaban kasar Nelson Mandela cikin kumari a lokacin da ya kai masa ziyarar barka da Kirsimeti a asibitin da aka kwantar da shi yau makonni biyu kenan.

Shugaba Zuma ya ce likitoci sun nuna gamsuwa da irin saukin da Mr. Mandelan ke samu, daga ciwon da ya yi fama da shi na huhu da kuma aikin tiyatar da aka yi masa.

A da an yi ta nuna fatan za a sallami Mr Mandelan mai shekaru casa'in da hudu, daga asibiti kafin kirsimeti, amma likitoci su ka ce har yanzu lokacin barinsa ya koma gida bai yi ba.

Karin bayani