Za a gudanar da zaben majalisar dokoki a Masar

Za a gudanar da zaben majalisar dokoki a Masar
Image caption Jami'an hukumar zaben Masar

A kasar Masar, nan da watanni biyu masu zuwa ne za a gudanar da zaben majalisar dokoki, bayan 'yan kasar sun amince da sabon kundin tsarin mulki.

Shugaba Mohamed Morsi ya sanya hannu a kundin tsarin mulkin, inda ya zama doka bayan hukumar zaben kasar ta sanar cewa kusan kashi biyu cikin uku na mutanen da suka kada kuri'a ne suka amice da shi.

Kashi daya bisa uku ne na yawan wadanda suka cancanci zaben suka kada kuri'a.

Daftarin tsarin mulkin ya haifar da tarzomar 'yan adawa a kasar wadanda suka yi zargin cewa kundin ya kunshi tanade-tanaden masu tsananin kishin Islama.

Sai dai shugaba Mursi da magoya bayansa sun ce sabon kudin tsarin mulkin zai kawo zaman lafiya a kasar.

Karin bayani