'Yan bindiga sun kashe mutane a Yobe

'Yan Sandan Najeriya
Image caption An kashe mutane a kauyen Piri

A Najeriya wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla mutane 5 tare da jikkata wasu, a wani hari da suka kai kan wata majami'a a kauyen Piri da ke kusa da garin Potiskum a daren jaji-berin ranar Kirsimeti.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a kauyen.

Galibin mazauna kauyen dai Kiristoci ne.

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jahar Lt. Eli Latharus ya tabbatarwa da BBC cewa ya zuwa yanzu sun yi nasarar cafke mutum guda da suke zargin yana da hannu a harin.

Mai magana da yawun rundunar tsaron hadin gwiwar ya kuma kara da cewar 'yan bindigar sun so shiga birnin Potiskum ne a jajiberin ranar Kirsimetin, amma hakan bai yiwu ba, daga bisani ne kuma yace su ka kaddamar da wannan hari akan majami'ar dake kauyen na Piri.

Karin bayani