Paparoma ya bukaci addu'ar zaman lafiya

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma ya yi jawabi a ranar Kirsimeti

Paparoma Benedict ya yi kiran da a zauna lafiya a duniya, a sakonsa na ranar Kirsimeti

Paparoman ya gabatar da jawabin ne daga barandar mujami'ar St Peter's dake Roma a gaban dubban masu ziyarar ibada.

Paparoman ya yayi kira ga Isra'ila da Palasdinawa da su sasanta, ya kuma la'anci kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Syria.

Ya kuma yi kira ga kasashen da su ka samu kansu cikin guguwar sauyin da ta ratsa ta kasashen Larabawa da su tabbatar da kafuwar adalci da mutunta al'umominsu.

Paparoma Benedict yayi fatan samun zaman lafiya a Najeriya, inda ya nuna takaici kan hare haren ta'addancin da ake kaiwa wanda a karo da dama yake karewa kan Kiristoci, ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin China da su yi la'akari da irin gudunmawar da addini zai bayar a cikin al'umarsu.

Karin bayani