Afghanistan: Bom ya tashi a sansanin sojin Amurka

Image caption Sojojin Afghanistan

Wani bom da ya tashi a sansanin sojin Amurka da ke gabashin Afghanistan, ya kashe wadansu masu gadi uku 'yan kasar sannan ya raunata mutane bakwai.

Wani kakakin kungiyar tsaro ta NATO ya ce masu tayar-da-kayar-baya ne suka tayar da bom a wata mota, a wani lamari da yake gani hari ne na kunar-bakin-wake.

Wani kakakin gwamnatin Afghanistan ya ce an kai harin ne a kofar sansanin sojin da ke Khost .

Yankin yana kusa da iyakar kasar da Pakistan kuma yana fama da karin hare-haren masu tayar-da-kayar-baya a kwanakin nan.

Karin bayani