Ayatollah Khamenei ya bude shafin facebook

Ayatollah Khamenei
Image caption Dubban jama'a ne suka kulla kawance da shafin jim kadan da bude shi

Wani abu da ya hada Fafaroma Benedict da sarauniya Elizabeth ta Ingila da jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, shi ne shafin sada zumunta na Facebook.

Shafin na Ayatollah ya samu dubban magoya baya sa'o'i kadan bayan bude shi.

Kimanin mutane dubu talatin ne ke magana akan shafin.

Kuma a tsarin facebook wannan na nuna adadin mutanen da ke tattaunawa kan shafin ko yada wani bayani ga abokansu daga shafin.

Sai dai wakiliyar BBC Karen Zarindast ta ce lamarin ya haifar da cece-kuce ganin cewa an haramta amfani da facebook a hukumance a kasar ta Iran.

Shafin Twitter da Instogram

An kawata shafin da hoton jagoran addinin na Iran yana matashi - lokacin juyin-juya halin kasar.

Hossein Ghazian wani masanin rayuwar dan'adam ne, kuma mai bin diddigin rayuwar Ayatoullahi Khameni, ya ce wannan na nufin Ayatoullahi na son tafiya da zamani:

"Tuni Ayatollah ya bude shafin Twitter da Instogram kafin ya shiga facebook - sai dai basu yi fice a Iran sosai ba - babu wanda ya damu da su sosai kamar facebook - a don haka shafin ya ja hankalin jama'a," a cewar Hossein Ghazian wani masanin rayuwar dan'adam kuma mai bin diddigin rayuwar Ayatoullahi Khameni.

Dubban jama'a ne suka kulla kawance da shafin nan take..sannan suka rinka bayyana ra'ayoyi masu nuna goyon baya da kuma a kasin haha.

Abin mamaki shi ne ba'a cire ko sako daya ba dake sukar Ayatoullah.

'Yan siyasa masu dabara kan yi amfani da irin wadannan maganganu wurin sanin aibin da ke faruwa a yankunansu da kuma jin ra'ayin jama'a.

Akwai dai wasu shafukan na sada zumunta da aka bude da sunan Ayatoullahi, amma ba a Hukumance ba.

Shi dai wannan shafin bai yi magana kan matsayin hukuma ba. Wani karin rudanin kuma shi ne jami'an Iran a lokuta daban-daban sun tabbatar tare da musanta cewa shafin na hukuma ne.

Karin bayani