An kalubalanci sakamakon zaben Ghana

Nana Akufo-Addo
Image caption Nana Akufo-Addo ya fadi a zaben shekara ta 2008 da kashi daya

Babbar jam'iyyar adawa ta Ghana ta shigar da kara a gaban kotun kolin kasar domin kalubalantar nasarar shugaba John Mahama a zaben farkon watan Disamban bana.

Jam'iyyar National Patriotic Party (NPP) ta yi watsi da sakamakon zaben na 7 ga watan Disamban, tana mai zargin tafka magudi.

Hukumar zabe ta ce Mr Mahama ya samu kashi 50.7% cikin dari, wanda ya bashi damar kaucewa zagaye na biyu da dan takarar NPP Akufo-Addo wanda ya samu kashi 47.7% cikin dari.

Masu sa ido na kasashen duniya sun ce an gudanar da zaben cikin adalci.

NPP ta ce ta yi nazari kan mazabu 26,000 inda aka kada kuri'u kusan miliyan 11.

Mr Akufo-Addo ya fadi a zagaye na biyu na zaben 2008 da kashi daya, sai dai ya amince da sakamakon.

Ana yiwa Ghana kallon daya daga cikin kasashen da suka ci gaba ta fuskar demokuradiyya a Afrika.

Karin bayani