'Sojoji sun kashe 'yan bindiga biyar a Kaduna'

Jihar Kaduna
Image caption Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da hare-hare a Najeriya

Jami'an tsaro a jihar Kaduna da ke Najeriya sun tabbatar da "rasuwar mutane biyar sakamakon bata-kashin da suka yi da wasu mutane a wani gida a unguwar Rigasa".

Mazauna unguwar Rigasa a jihar Kaduna sun shaida wa BBC cewa "an shafe sa'o'i ana harbe-harbe bayan da sojoji suka kai sumame wani gida a unguwar".

Rahotanni sun ce tun da misalin karfe hudu na asubahi ne ake ta bata-kashi tsakanin jam'ian tsaro da wasu mutane da ke zaune a cikin wani gida.

"Ban samu damar yin barci ba ko kadan saboda tsoro, karar harbe-harbe kawai muke ji kota-ina. Hakika hankalinmu ya tashi" kamar yadda wani mazaunin unguwar ya shaida wa BBC.

Jami'an tsaro sun ce sun kashe mutane biyar sannan suka cafke wasu guda biyu, sannan suka kara da cewa mutanen ne suka fara bude musu wuta lokacin da suka durfafi gidan.

Wakilin BBC a Kaduna Nura Muhammad Ringim, ya ce unguwar ta Rigasa ta yi kaurin suna wurin tashe-tashen hankula a baya.

Kuma an sha kai hare-hare kan jami'an tsaro da masu unguwanni a yankin, a cewar wakilin na mu.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren da a wasu lokutan ake alakanta wa da kungiyar nan ta Boko Haram.

Karin bayani