An sallami Mandela daga asibiti

Image caption Nelson Mandela

An sallami tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela daga asibiti, bayan ya kwashe kusan makonni uku a kwance sakamakon cutar huhu da ya yi fama da ita.

Wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar ta ce za a ci gaba da lura da Mista Mandela mai shekaru casa'in da hudu a gidansa da ke Johannesburg.

Sanarwar, wacce kakakin shugaban kasar, Mac Maharaj, ya karanta ta gidan talabijin na kasar ta kara da cewa ya kamata mutane su kyale Mista Mandela ya sarara domin a kula da lafiyarsa sosai.

Nelson Mandela shi ne shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko, kuma ana martaba shi a matsayin uban -kasa.

An dade ana nuna damuwa game a rashin koshin lafiyarsa.

Karin bayani