Brahimi ya nemi a kafa gwamnatin hadin kan kasa ta Syria

Brahimi da Shugaba Asad
Image caption Rikicin Kasar Syria

Wakilin Kasa da kasa ga Syria Lakhdar Brahimi ya yi kira da a kafa wata gwamnatin hadin kan- kasa ta Syria, wacce keda cikakken iko na zartarwa, har i zuwa lokacin da za' a yi zabe.

Yayinda yake magana a birnin Damashka, Mr Brahimi yace akwai bukatar a samu canji na zahiri, a kuma kawo karshen rikicin siyasar da akai kiyasin ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutum dubu arba'in da biyar

Wakilin BBC yace Lakdar Brahimi ya shaidawa manema labarai cewa Siriyawa na bukatar canji na hakika, amma sai dai abinda bai fayyace ba shine ko canjin na nufin saukar Bashar Al Asad daga mulki

Kalaman nasa dai, na zuwa ne a yayinda ma'aikatan diflomaciyar Kasar Syrian suka gana da jami'an ma'aikatar harkokin wajen Kasar Rasha a birnin Moscow.

Rasha dai tana goyan bayan gudanar da wata tattaunawa ta kasa, domin nemarwa kasar Syrian makoma

Karin bayani