'Yan jarida zasu samu 'yanci a Burma

Burma
Image caption 'yancin aikin jarida a Burma

A karon farko cikin shekaru hamsin Gwamnatin Burma ta bada sanarwar cewa za a kyale jaridun kasar masu zaman kansu damar gudanar da aikace aikacensu, kama daga watan Afrilu

Matakin dai ya biyo bayan soke aikin sa -ido akan aikace aikacen 'yan jaridun da gwamnatin kasar ke yi kai tsaye, kama daga watan na Afrilu

Dama an yi tsammanin wannan sanarwar, a irin sauye sauyen damukradiya da gwamnatin kasar take yi