'Dubban yara na fuskantar hadari a Congo'

Dubban yara na fuskantar barazana a Congo
Image caption Tambarin kungiyar Save the Children

Kungiyar bayar da agaji ta Save the Children ta yi gargadin cewa dubban yaran da rikici ya raba da iyayensu na fuskantar matukar hadari yayin da iyayen na su ke gujewa rikicin da ake yi a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Kungiyar ta yi wannan gargadi ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a, tana mai yin kira da a dauki matakan gaggawa don ceto yaran daga halin da suke ciki.

A cewar kungiyar, a halin da ake ciki dubban wadannan yara ne a gabashin Congo ke fuskantar matukar hadari na yin lalata da su, ko sace su, ko ma a sanya su cikin kungiyoyin 'yan tawaye.

Kungiyar bayar da agajin ta ce tana hadin gwiwa da wadansu kungiyoyi, kana suna taimakawa wajen gano dubban yaran da yakin ya raba da iyayensu, inda kuma suke daukar matakai na gano iyayen na su, domin sake hada su waje guda.

Yaran suna cikin firgici

Da dama daga cikin yaran da yakin ya raba da iyayensu na zaune ne a sansanonin da ke warwatse, don haka ba su ma san abin da ke faruwa da iyayen na su ba.

Kusan irin wadannan yara miliyan daya ne ke zaune a lardin arewacin Kivu, bayan yakin da aka yi a baya bayan nan tsakanin 'yan tawaye da dakarun Congo ya raba su da iyayensu.

Babban jami'in kungiyar a kasar Congo, Rob Mac-Gillivray, ya ce akasarin yaran da suka gano, na cikin mummunan hali na firgita, kuma ba su ma sani ba ko iyayensu na da rai, ko kuwa an kashe su.

Ya kara da cewa kugiyar ta gano yara 923 a wuraren da yakin ya yi kamari, lamarin da ya sanya take fargabar cewa akwai dubban irin wadannan yaran a sassa daban-daban na arewacin Kivu.

Ta yi fatan cewa za a gano iyayen dubban wadannan yaran don su koma rayuwar da suka saba da ita gabanin yakin.