Obama zai gana da 'yan majalisa a kan kasafin kudi

Image caption Barack Obama

Shugaban Amurka Barak Obama ya gayyaci shugabannin majalisar dokokin kasar domin su tattauna a fadar White House ranar Juma'a game da kasafin kudi don kaucewa matsalar kudi.

Kwanaki hudu ne kawai suka rage ga 'yan jamiyyar Republican da na Democrat domin su cimma yarjejeniya ko kuma a kara haraji da zaftare biliyoyin dala da gwamnati ke kashewa.

Shugaba Obama ya dakatar da hutunsa ne a Hawaii ya dawo Washington domin a ci gaba da tattaunawa.

Abu ne mai wuya a cimma matsaya a kan lamarin kafin sabuwar shekara.