Obama zai gana da 'yan majalisa akan rikicin kasafin kudi

Obama
Image caption Rikicin kasafin kudi a Amurka

Shugaba Obama zai gana da shugabannin 'yan majalisar dokokin Kasar a fadar White house cikin wasu 'yan sa'oi masu zuwa, a kokarin cimma yarjejeniya ta karshe domin hana kasar fantsama cikin rikicin kasafin kudi

Amma sai dai akwai shakku da ake cigaba da nunawa game da yiwuwar za a iya kaucewa kara kudaden harajin da kuma zaftare kudaden da ake kashewa a Kasar kafin sabuwar shekara.

Akwai fargabar da ake na cewa rikicin kasafin kudin ka iya jefa Amurka cikin wani rikicin tattalin arzikin haka kuma hannayen jari sun fadi a nahiyar turai da kuma kasuwannnin Amurkar

Karin bayani