An haramtawa Amurkawa daukar marayu 'yan Rasha

Shugaba Putin
Image caption Cece kuce akan daukar marayun Rasha

Shugaba Putin na Rasha ya sanya hannu akan dokar nan da ake cece kuce akanta wacce ta haramtawa Amurkawa daukar 'ya'yan Rashawa marayu.

Haramcin wani martani ne ga wata dokar Amurka wacce ta kara tsaurara takunkumi akan jami'an Kasar Rashan da ake zargi da cin zarafin bil adama.

Amurkar dai ta zafafa wannan doka ne bayan mutuwar wani lauya Sergei Magnisky-- a wani gidan kurkukun Kasar Rashan shekaru uku da suka gabata.

Wata kotu a birnin Moscow ta dai wanke Jami'in da ake zargi da mutuwar lauyan, jim kadan kafin Mr Putin ya sanya hannu kan dokar data haramtawa Amurkawar daukar marayun Kasar

Karin bayani