Obama na da kwarin gwiwa game da zartar da kasafin kudi

Barack Obama

Shugaba Barack Obama ya ce yana da kwarin gwiwa za a iya cimma matsayar da za ta kare Amurka fadawa cikin matsalar kasafin kudi kafin wa'adin ranar farko ta sabuwar shekara.

Sai dai ya yi gargadin cewa Amurkawa sun fara kosawa da kika-kakan da ake ciki.

Mista Obama ya bukaci a dauki matakin gaggawa a kan lamarin.

Idan dai ba a kai ga cimma matsaya ba, Shugaba Obama ya ce zai so majalisar dokokin ta kada kuri'ar samar da wani shiri da zai kare matsakaitan iyalai daga karin haraji.

Karin bayani