Jirgin sama ya yi hatsari a Moscow

Hadarin jirgin Moscow
Image caption Hadarin Jirgin Moscow

Wani jirgin sama ya yi hadari a Rasha bayanda ya shallake titin saukarsa a filin jiragen sama na Vnukovo da ke Moscow.

Jirgin ya rusa katangar filin sannan kuma ya kama da wuta.

Daga nan kuma sai ya karye gida uku.

Mahukunta sun ce akalla mutane hudu ne suka rasu.

Mutane takwas ne dai a cikin jirgin saman fasinjan samfurin Tupolev-204 mallakar kamfanin Red Wings.

A lokacin da jirgin ya yi hadari ana yayyafin dusar kankara sai dai ba'a san abinda ya haddasa hadarin ba.

Karin bayani