An yi jana'izar 'yar Indiyan nan da aka yiwa fyade

Akwatin gawar 'yar Indiyar da aka yiwa fyade
Image caption Akwatin gawar 'yar Indiyar da aka yiwa fyade

A yau da hantsi ne aka yi jana'izar 'yar Indiyar nan da aka yi wa fyade a motar haya a Delhi, babban birnin kasar.

Manyan jami'an Indiya da makusantan marigayiyar ne suka halarci wurin da aka kona gawar.

Lamarin dai, ya fusata al'ummar kasar tare da haddasa zanga-zanga a birane da dama.

Bayan da rikici ya barke yayin zanga-zangar a wasu wurare, 'yan sanda sun rufe wasu sassan Delhi tare da wasu tashoshin jiragen kasa.

An dai tuhumi mutane shida da laifin yi mata fyaden kuma su na fuskantar hukuncin kisa idan kotu ta tabbatar da laifinsu

Gwamnatin Indiya dai ta sha alwashin hukunta masu fyaden cikin gaggawa sabanin jan kafar da aka saba yi a irin wadannan shari'o'in a baya, kana kuma zata dauki matakan kare hakkin mata a kasar.