Maganin tari ya kashe mutane sama da 30 a Pakistan

Gurbataccen maganin tari a kasar Pakistan
Image caption Gurbataccen maganin tari a kasar Pakistan

Hukumomi a kasar Pakistan na bincike kan mutuwar mutane fiye da 30 cikin kwanaki ukkun da suka gabata, da ake zargin sun mutu ne sakamakon shan wani gurbataccen maganin tari

Mutanen wadanda yawancinsu sun fito ne daga birnin Gujranwala dake gabashin kasar, da wasu yankunansa an ce dama sun yi suna wajen tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Ana dai kyautata cewar mai yiwuwa sun sha da yawa ne don ya sanya su maye.

Likitan wata asibitin a yankin ya ce mutane sama da hamsin ne masu wannan matsalar suka kwanta asibitin.

Wasu gwaje-gwaje sun nuna cewar an gano birbishin wani sinadari wanda ke da matukar hadari ga bil-adama.