An samu gawarwakin mutane 21 da aka sace a Pakistan

Taswirar kasar Pakistan
Image caption Taswirar kasar Pakistan

Hukumomi a kasar Pakistan sun ce gawarwakin mutane ashirin da dayan da wasu 'yan bindiga suka sace a ranar Alhamis, a yankin arewa maso yammacin kasar.

An gano gawarwakin mutanen da aka yiwa horon soji ne, an yi musu fata-fata da harsasai a cikin kilomitoci hudu na sansanin dake bayan birnin Peshawar yankin da aka sace sun.

Wani jami'i a yankin ya ce sai da aka daddaure hannayen su kafin a harbe su.

An ba da rahoton cewar mayaka na kungiyar Taliban sun ce sune ke da alhakin sace mutanen, lokacin da ma sai da aka kashe 'yan sanda biyu, aka kuma raunata na ukku.