Obama na son rage bindigogi a Amurka

'Yan bindiga na kashe yara a Amurka
Image caption 'Yan bindiga na kashe yara a Amurka

Shugaba Obama yace ya na fatan ganin an amince da dokar takaita amfani da bindiga a cikin shekara mai kamawa.

Mr. Obama ya kuma shaidawa wani gidan talabijin a Amurka cewa bai yadda da shawarar kungiyar masu amfani da bindigogi cewa baiwa masu gadin makarantu bindigogi shi zai hana kashe kananan yaran da basu yiwa kowa laifi ba.

Yace: "Ban amince wai mafita kadai ita ce kara yawan bindigogi a makarantu ba. Kuma ina jin mafi yawan Amurkawa ma ba su amince hakan zai iya warware matsalar ba. Kaga babu yadda zamu cimma wannan manufa har sai al'ummar Amurka sun amince ta na da muhimmanci".

Mr. Obama dai ya nada wani kwamitin karkashin jagorancin mataimakinsa Joe Biden domin fito da dabarun takaita mallakar bindiga a Amurka, bayan da wani dan bindiga ya hallaka mutane 26 mafi yawansu kananan yara a garin Newtown.

Karin bayani