Hillary Clinton na fama da daskarewar jini

clinton
Image caption Hillary Clinton

Ana yiwa sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, maganin daskarewar jini a wani asibitin New York.

Maganin shi ne na baya bayanannan a jerin matsalolin rashin lafiyar da take fama da su.

Yanzu haka likitoci na ba ta magungunan tsinka jini kuma za su ci gaba da sa ido a kanta har zuwa talata.

Ranar Lahadi ne aka gano Misis Clinton din na da matsalar daskarewar jinin lokacin da ta je a duba lafiyarta bayan da a farkon wannan watan ta suma.

An dangata faduwar da ta yi da wani ciwon cikin da ta samu sakamakon matsanancin rashin ruwa a jikinta.

Karin bayani