Isra'ila ta soma bari a shigar da kaya cikin Gaza

gaza
Image caption Motocin daukar kaya sun soma shiga zirin Gaza

Isra'ila ta tabbatar cewa ta fara bari ana shigar da kayayyakin gini cikin zirin Gaza wanda aka hana shigarawa da dadewa a karkashin datsewar da Isla'ila ta yiwa yankin.

Matakin bari a shigar da kayan wani bangare ne na yarjejeniyar da ta kawo karshen fadan kwanaki 8 din da aka gwabza tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a watan Nuwamba.

Wani kakakin sojin Isra'ila ya ce za'a ci gaba da tura kayayyyakin idan har kan iyakar dake tsakanin Isra'ilan da Gaza ta kasance ba wani tashin hankali.

Wani jigon Palasdinawa Raed Ghalban ya ce abin da Isra'ila ke bari a shiga da shi bai isa a sake gina zirin Gaza ba.

Ya kara da cewar "abubuwa kadan ne, kuma har yanzu akwai kayan gini da ba'a yadda a shiga da su ba kamar karfe da siminti".

Karin bayani