Ban kadu ba a kan tattalin arziki -Morsi

morsi
Image caption Shugaban Masar, Muhammed Morsi

Shugaban kasar Masar, Muhammed Morsi ya ce bai kadu da faduwar da darajar kudin kasar ya yi ba, wanda ba'a taba ganin irinsa ba.

Kafar yada labaran kasar ta rawaito shugaba Morsi na cewa cikin 'yan kwanaki yanayin zai daidaita.

Furicin na sa ya zo a dai dai lokacin da babban bankin kasar ya kaddamar da wani tsari na gwanjan kudadan waje ga bankunan kasar domin kokarin dai daita darajar kudin Masar.

Da yawan Misirawa na ta canza kudin kasarsu zuwa dalar Amurka bisa fargabar faduwar darajarsa.

Shugaba Morsi ya lashi takobin daidaita tattalin arzikin kasar.

Karin bayani