Majalisar Dattawan Amurka za ta yi zama na musamman

Rage kashe kudaden gwamnati a Amurka
Image caption Rage kashe kudaden gwamnati a Amurka

Majalisar Dattawan Amurka za ta yi zaman na musamman, a yunkurin ta na kaucewa dokar rage kudaden da gwamnati ke kashewa, da kuma karin kudaden haraji.

Yan siyasar dai na kokarin ganin cewa tattalin arzikin Amurka bai durkushe ba.

Hakan dai ya biyo bayan yarjejeniyar da aka yi tsakanin 'yayan jam'iyar Republicans da na Democrats, a cikin shekara ta 2011 na su jingine daukar matakai game da batun rage kashe kudaden har ya zuwa karshen shekara ta 2012.

Ana dai sa ran membobin majalisar da suka samu zazzafar rarrabuwar kawuna a Amurkar zasu sake wani zama ne a yau.

Wannan na zuwa yayin da ake tsakiyar wani yunkurin karshe na kaucewa shirin zaftare yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, wanda zai fara aiki daga ranar daya ga watan Janairu.

Ana kuma sa ran 'yan Majalisar Dattawan Amurkar za su yi wani zama na ba kasafai ba da 'yan majalisar wakilai.

Masana harkokin tattalin arziki dai sun ce wannan mataki zai iya sake durkusar da tattalin arzikin Amurka.

Sai dai shugaba Barack Obama ya ce har yanzu akwai lokaci na daukar matakai.

Mr Obaman ya ce idan aka ture batun banbance-banbancen siyasa ko ra'ayi, abu mafi muhimmanci dake gaban gwamnatinsa shine tabbatar da cewa haraji kan matsakaitan iyalai ba zai karu ba, ta yadda zai shafi tattalin arziki.

Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin karewar shirin zaftare kudaden da haraji na zamanin tsohon shugaban Amurka George W Bush, wato ranar jajiberin sabuwar shekara.