China ta jaddada ikonta kan kafofin watsa labarai

Yanjarida masu zanga zanga a China
Image caption Yanjarida masu zanga zanga a China

Masu zanga zanga sun gudanar da gangami a rana ta biyu a birnin Guangzhou dake kudancin China, domin nuna goyan baya ga 'yan jarida wadanda suke nuna rashin amincewar- su, dangane da batun tace labaransu.

Wakilin BBC yace wasu daga cikin masu zanga zangar sun rufe fuskokinsu, wasu kuma na dauke da furanni, domin nuna juyayin abinda suke kallon mutuwar 'yan cin aikin jarida ne

Jaridu a daukacin Chinan dai sun buga wani sharhi da jam'iyyar Komunusanci ta basu umarnin sun wallafa, wanda ya jaddada mahimmancin ikon da gwamnati ke da shi akan kafofin yada labaru

Sai dai Wasu jaridu sun ki wallafa wannan sharhin, wasu kafofin labarai na shafin Intanet ma, sun nisanta kansu da abinda sharhin ya kunsa

Yan mutane kalilan yawancin su matasa sun bayyana a rana ta biyu a ofishin mujallar ta South Weekly wadda ake wallfawa mako mako.

Wasu daga cikinsu sun rufe fuskokin su da kyallaye suna kuma dauke da furanni domin jimamin abin da suke gani a matsayin kashe yancin yan jarida a daya daga cikin birane mafi sakar mara a kasar China.

An ruwaito aukuwar zazzafar muhawar da jayayya a lokacin da magoya bayan jam'iyyar kwamunisanci dauke da tutoci su ma suka bayyana a wurin.

Wannan takaddamar dai ta zamo jigon muhawara game da yancin samun bayanai a China kuma zakaran gwajin dafi ga sabbin shugabannin da suka karbi ragamar mulki a bara.

Karin bayani