Kungiyar kwadago ta duniya ta yi gargadi game da ma'aikata 'yan aikin gida

Babban taron kungiyar kwadago ta duniya a Geneva
Image caption Babban taron kungiyar kwadago ta duniya a Geneva

Kungiyar kwadago ta duniya - ILO ta ce an tsame mafi akasarin 'yan aikin gida daga kariyar da ya kamata ace ana baiwa ma'aikata, kuma ana cin zarafinsu da kuma yin lalata da su.

A wani rahoto irinsa na farko da kungiyar ta fitar, ILO tace kashi goma cikin dari na 'yan aiki kadai, suke amfana daga irin wannan kariya kamar sauran ma'aikata.

Wakiliyar BBC ta ce Kungiyar tayi kiyasin cewa akwai 'yan aiki fiye da miliyan hamsin a duniya, kuma mafi akasarinsu mata ne

Kungiyar kwadagon dai ta samar da wasu dokoki na baiwa 'yan aikin kariya, amma ya zuwa yanzu kasashe uku ne kawai suka rabbata hannu akan dokokin